Karashen Zabe: EFCC ta tura ma’aikata 100 a Kano, Katsina da Jigawa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC), ta ce ta tura jami’anta guda 100 domin yaki da sayen kuri’u a Kano, Katsina da kuma Jigawa a yayin zaben da za a yi ranar Asabar a jihohin.

 

Kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano, Farouk Dogondaji ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kano ranar Juma’a.

A karo na biyu: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara

“Mun tura jami’ai 20 domin sanya ido kan yadda zaben ‘yan majalisar jiha ke gudana a Kafur, Kankara a jihar Katsina,” inji shi.

 

FCE Bichi na daf da durkushewa, saboda matsalolin da suka yi yawa a makarantar – Dr. Hussaini Peni

Ya kuma bayyana cewa an kuma tura isassun ma’aikata domin sanya ido kan aikin zaben a mazabar Tudun Wada/Doguwa, da Takai da kuma wasu zabukan ‘yan majalisar jiha da za a gudanar a jihar Kano.

 

Dogondaji ya ce an kuma tura wasu ma’aikatan domin Sanya idanu a zabukan ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar a Katsina da Jigawa, domin hana sayen kuri’u.

 

“Zamu fito fili a dukkan runfunan zabe a Kano, Katsina da Jigawa domin sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da zabe a lokacin zaben da kuma bayan zabe.

 

Dogondaji ya yi kira ga ma’aikatan da su kasance masu kwazo da kwarewa wajen gudanar da ayyukan da aka ba dora musu.

 

Ya shawarci iyaye da kada su bari a yi amfani da ‘ya’yansu wajen yin bangar siyasa, domin duk wanda aka samu yana yi za a kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...