Daga Sani Idris Maiwaya
Zababben gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sake baiwa shugabannin kananan hukumomin jihar kano 44 da sauran manyan ma’aikatansu shawarar kada su kuskure a yi amfani da kudaden kananan hukumomin kan zaben da za’a sake a wasu yankuna a jihar.
“Mun da cikakkiyar masaniyar cewa gwamnati Mai barin gado tana shirin fitar da kudada kusan naira Miliyan sittin- sittin zuwa sama domin a yin amfani da su wajen dauko yan daba don su tada hatsaniya a yayin zaɓukan da za a sake a wasu kananan hukumomi a Kano”. A cewar Sanusi Bature
FCE Bichi na daf da durkushewa, saboda matsalolin da suka yi yawa a makarantar – Dr. Hussaini Peni
Babban Sakataren yada labaran zaɓaɓɓen gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Bayan karbar Sammaci, Rarara ya gurfana a gaban kotu
Yace suna kira ga duk shugabannin kananan hukumomi musamman na Nasarawa da Doguwa da su kiyake bada kudaden saboda gwamnati Mai jiran gado bazata lamunci barnatar da kudaden al’umma ba gaira ba dalili ba.
” Ina sanar da duk wadanda wannan shawarar ta shafa da su sani cewa duk wanda ya bari aka fitar da kuɗi da sanin sa to ya Sani zamu daukin matakin ladabtarwa akan sa don haka sai a kiyaye, idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira”. Inji Sanusi Bature