‘Yan takarar majalisar jiha na NNPP su 9 a Kano sun yi karar APC, INEC a Kotun sauraren kararrakin zabe

Date:

Daga Fatima Kabir Labaran

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jihar da ke zamanta a harabar kotun Miller Road da ke Kano ta karbi koken ‘yan takarar majalisar dokokin jihar su 9 na jam’iyyar NNPP Inda suke karar jam’iyyar APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Masu shigar da karar sun kuma roki kotun da ta amince da bukatarsu ta neman a basu dama su duba kayan da hukumar zabe ta yi amfani da su a zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga Maris, 2023.

Zaɓen Gwamnan Kano: APC ta roki kotun sauraren kararrakin Zabe har abubuwa guda 5

Sun kuma bukaci bayan kotun ta bada izinin duba kayan, ta ci gaba da gudanar da shari’ar akan karar da suka shigar.

 

Abubuwan da dokar majalisar masarautun jihar kano ta kunsa

Sannan kuma masu karar na jam’iyyar NNPP sun shigar da karar ne a gaban kotu domin kalubalantar batutuwan da suke ganin sun sabawa tanadin dokar zabe ta 2022.

 

‘Yan takarar jam’iyyar NNPP da suka shigar da karar INEC da APC a kotun sauraren kararrakin zabe, sun hada da, Aminu Saidu Ungogo, Isiyiaku Ali Danja, Abdullahi Ali Wudil Manager, Kabiru Getso Haruna, Mahmud Tajo Gaya, Abdullahi Iliyasu, Musa Adamu Ahmad, Aminu Ibrahim Dambatta, Abdu Ibrahim Madari.

Jaridar AUTHORITY ta bayar da rahoton cewa, an shigar da karar ne a gaban kotu, a ranar 4 ga Afrilu, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...