Karashen Zabe: Zamu samar da ingantaccen tsaro a Kano – Kwamishinan Yan Sanda

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta baiwa mazauna jihar tabbacin samun isasshen tsaro a yayin zaben da za a gudanar a jihar a ranar 15 ga watan Afrilu.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan zaben da za a karasa, wanda aka gudanar a ofishin INEC da ke Kano ranar Laraba.

 

Mamman Dauda wanda Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, Mu’azu Mohammad, ya wakilta, ya ce tuni ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar suka tsara tsarin tsaro da ya dace da nufin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Zaɓen Gwamnan Kano: APC ta roki kotun sauraren kararrakin Zabe har abubuwa guda 5

 

CP Dauda ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar na kokarin ganin an gudanar da zabe ba tare da rikici ba.

 

Rashin wuta: Yan KEDCO ya kamata ku nemi aljannar ku a wanann wata na Ramada – Falakin Shinkafi

Ya bayyana cewa tuni aka ba da wani ingantaccen odar aiki kan yadda za a samar da tsaro a duk runfunan zabe ga jami’an da aka tura domin gudanar da aikin.

 

Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su gargadi magoya bayansu da su guji yin duk wani abu da zai kawo tashin hankali kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.

 

A nasa bangaren, kwamishinan zabe na jihar, Amb. Abdu Zango, ya ce duk da cewa an gudanar da zabukan shugaban kasa da na gwamnoni cikin kwanciyar hankali a Kano, wasu mazabu na tarayya da na Jihohi an sami kalubalen da ya sa za’a sake zaben.

 

Ya ce wasu daga cikin rumfunan zabe da abin ya shafa inda za a sake gudanar da zaben sun hada da kananan hukumomin Danbatta, Makoda, Dawakin Tofa, Gabasawa da Gezawa.

 

Sauran sun hada da Gaya, Takai, Garko, Wudil, Warawa, Ungogo, Ajingi, Gwarzo, Tudun Wada da Fagge.

 

Zango ya tabbatar da aniyar INEC na tabbatar da sahihin zabe a wuraren da za’a sake zabukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...