Abubuwan da dokar majalisar masarautun jihar kano ta kunsa

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi wa dokar majalisar masarautun jihar Kano gyare-gyare .

 

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar kiru Hon. Kabiru Hassan Dashi wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar ta Kano ya shaida wa BBC abinda sabbin dokokin suka ƙunsa.

 

Kabiru Dashi ya ce dokokin guda biyu ne, ɗaya gyara aka yi mata, yayin da ɗayar kuma sabuwa ce.

 

Rashin wuta: ‘Yan KEDCO ya kamata ku nemi aljannar ku a wanann wata na Ramada – Falakin Shinkafi

Ya ce dokar da aka yi wa gyaran ita ce dokar majalisar masarautun jihar, inda dokar ta tanadi rage adadin mambobin majalisar masarautar daga 30 zuwa 17.

 

Sannan kuma ya ce daga cikin gyare-gyaren dokar, daga yanzu kwamishinan ‘yan sandan jihar da shugaban hukumar DSS na jihar da shugaban hukumar tsaro ta Civil Defence, da kuma shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin jihar, duk suna cikin mambobin majalisar masarautun jihar.

Zaɓen Gwamnan Kano: APC ta roki kotun sauraren kararrakin Zabe har abubuwa guda 5

 

A gefe guda kuma Hon. Kabiru ya ce an samar da sabuwar doka kan masarautun Gaya da Ƙaraye da kuma Rano, inda a yanzu sabuwar dokar ta tanadi cewa dole sai ‘yan asalin gidan masarautun ne kawai za su yi sarauta a masarautun.

 

”Kamar dai yadda yake a masarautun Kano da Bichi inda doka ta tanadi cewa dole sai ‘yan gidan Dabo ne kawai za su yi mulki a masarautun”, in ji shi.

 

Dan majalisar ya ce su ma masarautun Gaya da Ƙaraye da Gaya an zaƙulo wasu mutane waɗanda tun asali su ne suke mulki a masarautun.

 

”Yanzu misali kamar gidan sarki Gaya akwai gidan Abubakar Sayyadi, gidan sarautar Rano kuma akwai sarki Ila, gidan Karaye kuma akwai gidan sarki Alu”, in ji shi

A cewarsa waɗannan su ne gidajen da dokar ta ce dole sai waɗanda suka fito daga tsatson gidajen ne kawai za su riƙe sarautar masautun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...