Daga Abdulrashid B Imam
Shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari zai tafi Saudiyya ranar Talata a wata ziyara ta karshe da zai kai wata ƙasar waje a matsayin shugaban ƙasa.
Akalla Shugaba Buhari zai shafe kusan mako guda daga ranar 11 ga watan Afrilu zuwa 19 ga wata.
Ƙasar Ingila za ta dakatar da daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Najeriya
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar, ta ce Muhammadu Buhari zai kuma gudanar da aikin Umrah yayin ziyarar tasa.
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya yiwa Alhaji Aminu Dantata Ta’aziyyar Rasuwar Matarsa
Sanarwar Mallam Garba Shehu ta kuma ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan mukarraban gwamnatinsa a wannan ziyara zuwa kasar Saudiyyan.