Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban sashin fasahar sadarwa na darikar Tijjaniyya na kasa Dr. Ali Tamasi ya yi kira ga matasa maza da mata da su dage wajen yin ibada a goman ƙarshe ta wannan wata na Ramadan.
” Ku kashe datar wayoyin ku ku Kuma nisanci tv da Kuma kwallon kafa domin ku Kara samun kusanci da mahaliccin ku shi ne Allah don samun falalar dake cikin goman ƙarshe ta wannan wata na Ramadana mai alfarma”. Inji Dr. Tamasi
Rarara ya raba kayan abinchi ga magidanta a garin kahutu
Dr . Tamasi ya bayyana hakan ne yayin wata lacce da ake gabatarwa a zawiyatu ahlil faidhatul Tijjaniyya dake gidan Alhaji Uba Ringim a birnin kano.
Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa
Yace hakan zaba ta basu damar gudanar da karatun alkur’ani da ambaton Allah da yiwa Annabi S A W salati da sauran ibadun da Allah yake so, don inganta duniya da lahirarsu.
” Babbar matsalar matasan wannan zamani ita ce wadancan abun da na lissafa , kuma babu shakka da zasu hakura da su a wadannan kwanakin to da sun ribaci falalar dake cikin kwanakin tunda basu da tabbacin za su sake riskar azumin watan Ramadan”. Dr. Tamasi