Nazari: Ilimi zai kara samun gata a Zamfara kasancewar Dauda Dare ya zama Gwamnan Jihar – Sadeeq Muhd

Date:

Daga Sadeeq Muhammad Fagge.

 

Wani Matashi dake nazari akan al’amuran da suka shafi harkokin ilimi, yayi hasashen cewa Ilimi zai kara inganta a jihar Zamfara kasancewar wanda ya zama sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Dr. Dauda Lawan dare mutum ne da yasan darajar Ilimi.

 

Babu shakka idan zakai nazari akan mutum matukar kana so kayi masa adalci to dole ka Kalli abubuwan da yayi a baya, wanda su ne zasu baka damar hasashen abun da zai iya yi a gaba musamman idan ya Sami wata dama fiye da wacce yake da ita a baya.

 

Zan dan waiwayi baya, don in tunasar da masu karatu irin hidimar da mahaifin Dauda ya yiwa al’ummar jihar Zamfara.

 

Kamar dai mahaifinsa, Dr Dauda Lawal Dare ya shahara wurin taimakon al’umma.

 

1) A jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau, wato (Federal University Gusau) ya gina:

Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da dalilan da suka sa kudin hajjin bana ya yi tashin gwaron zabi

– Hanya mai nisan kilomita uku da rabi, da
kofar tsaro.

2) A kwalejin aikin jinya da ungozoma dake Gusau wato (College of Nursing and Midwifery, Gusau)

– Ya gina dakin kwanan dalibai mata mai gadaje 350 da saka dukkanin kayayyakin da ake bukata.
– Ya gina dakin kwanan dalibai na maza mai gadaje 250 tare da dukkanin kayayyakin da ake bukata
– Shine ya biya kuddin tantancewa da amincewa da makarantar (accreditation fees)

3) A Makarantar Fasaha ta Lafiya dake Tsafe, wato (College of Health Technology, Tsafe)

 

Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa

– Ya gina rukunin ingantattun ajujuwa guda hudu.

4) A cikin birnin Gusau ya gina:

– Masallatai da dama da makarantun Islamiyya, ya inganta makabartu zuwa na zamani masu dauke da kayan aiki na zamani.

Taimakon sa bai kare a Zamfara ba:

5) A kwalejin ‘yan sanda, Kaduna,

– Ya gina ingantattun rukunin ajujuwa
– Ya gina Masallacin Juma’a a Police College
– Ya gina ajujuwan Islamiyya da dama dake kewayen Kaduna.

6) A Makarantar Sakandaren Gwamnati dake Kachia, wato (Government Secondary School, Kachia)

– Ya gyara rukunin azuzuwa tare da saka kayayyakin koyarwa
– Ya gina zaure na koyarda na’urar kwamfuta a makarantar.
– Ya gina masallacin Juma’a a ITN Zaria.
– Ya kuma gyara shahararren masallacin Juma’a na tashar jirgin kasa a jihar Kaduna.

7) A Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda yayi karatu:

– Ya gina bene mai hawa uku wanda ya kunshi azuzuwan karatu da ofisoshin ma’aikata,
– Ya bada sabuwar mota kirar bas ga political science department,
– Ya bada mota kirar Jeep SUV ga HOD na political science department.

8) A Jami’ar Usman Danfodio dake Sakkwato

– Ya kuma gina rukunin ajujuwa da kayan aiki a sashen ilimin likitanci na Jami’ar ta Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.

9) A garin Guga jihar Katsina (Garin Mahaifiyarsa) Dr Dauda Lawal Dare:

– Ya gina Cibiyar Kiwon Lafiya a matakin Farko (Primary healthcare center) na garin

– Ya gyara makarantun garin
– Ya gina zaure na koyon na’urar kwamfuta.
– Ya kuma samar da ruwan sha ga daukacin al’umma ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana

10) Dauda ya kafa:

– Zam blocks, babbar masana’antar block a Zamfara.
– Ya kafa Zam rice Mills
– Ya kafa Ruwan Azuma
– Ya kafa Zam agrochemical (babban kamfanin hada taki a duk Arewacin Najeriya)

11) Dauda ya dauki nauyin daukar ’yan asalin jihar Zamfara su 120 don yin karatun digiri daban-daban a jami’ar Iheris da ke Togo karkashin Gidauniyar Dokta Dauda Lawal a fannoni daban-daban da suka hada da:

– Computer engineering
– Information technology
– Public administration
– International relations
– Human resources management, and
– Computer science.

Wannan Yana Nuni da Cewa Dauda Lawal Dare Hadimin Al’umma ne,tun a lokacin baya zuwa yanzu da Yasamu dama ta musamman da za’a kara Habbaka harkar ilimi a jihar zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...