Ba a son raina zakara ya haɗa ni faɗa da makwabcina ba – Mai zakaran da kotu ta ce a yanka

Date:

Daga Umar Usman Sani mainagge

 

Mamallakin zakaran da aka zartar wa da hukuncin kisa a jihar kano, ya ce bai ji daɗin yadda marigayin zakaran da ya haɗa shi faɗa da maƙwabcinsa ba.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 a ranar talatar da ta gabata ta rawaito, Mai shari’a Halima Wali a wata kotu da ke Kano ta yanke wa zakaran hukuncin kisa, Inda ta bada umarnin ga mai zakaran da ya yanka shi .

 

Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da dalilan da suka sa kudin hajjin bana ya yi tashin gwaron zabi

Matakin dai ya zo ne bayan wasu maƙwabtan mai zakaran biyu suka shigar da ƙara, inda suka zargi zakaran da hana su sakat saboda yawan caran da yake yi da zarar sanyin asuba ya kaɗa.

 

Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa

A tattaunawarsa da kafar yada labarai taBBC, mai zakaran, Isiyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin Kano, ya ce bai taɓa samun saɓani da makwabcinsa ba a tsawon shekara 20 sai a dalilin zakaran nasa

 

Yadda ta kasance kenan da zakaran da kotu ta yankewa hukuncin kisa

“Ba zan yi kewar zakaran ba, saboda ba wata shaƙuwa ta ƙut-da-ƙut muka yi da zakaran ba”. Inji mai zakaran

 

“Yara ne ma suka yanka rigimammen zakaran kafin ma na dawo gida a ranar Juma’a”.

 

Tun farko, ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙarar, Yusuf Muhammad, ya ce carar da zakaran ke yi, tana shiga haƙƙinsa don kuwa ba ya samun barci cikin kwanciyar hankali da lumana.

 

Isyaku Shu’aibu ya faɗa wa kotun cewa da ma ya sayi zakaran ne don bikin Easter, inda ya buƙaci kotun ta yi masa rangwame zuwa ranar Juma’a kafin zartas masa da hukunci don amfani da naman a ranar Good Friday, hakan tasa kotun ta amince da bukatar ta shi.

 

Rahotannin da kadaura24 ta samun sun tabbatar da cewa tuni aka yanka zakaran da Kotun ta bada umarnin yanka shi a ranar juma’ar data gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...