Daga Rabilu Muhammad Kano
Zababban dan majalisar tarayya na karamar hukumar Nasarawa a jihar kano Hon. Hassan Shehu Hussaini (HASH) ya gwangwaje wasu matasa guda biyu da Sabbin babura kirar Bajaj.
Sabon dan majalisar ya mikawa matasan baburan ne su ne a jiya 2 ga watan Mayu, 2023 kafin a ce an rantsar da shi a matsayin Dan Majalisar karamar hukumar.
Jarumar Nollywood, Mercy Aigbe, ta Musulunta
A lokacin da yake mika mu su mashinan, Hassan Shehu ya bayyana cewa al’ummar Nasarawa su sani cewa wannan somin tabi ne ga al’ummar karamar hukumar kafin su shiga ofis.
Yanzu-Yanzu: Ganduje ya kafa kwamitin mika mulki mai mutane 17
Kuma yana kira da al’umma da su taya shi da addu’a domin ganin ya gudanar da ayyukan cigaba ga al’ummar Nasarawa wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar su.