Gwamnatin jihar Kano ta ce tana maraba da duk wata adawar siyasa mai tsafta wadda za ta haska mata wasu ayyuka da za ta bijiro da su don ciyar da jihar gaba.
Kwamishinan Yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da kwamatin Iyayen kungiyar Yan gwagwarmaya masu magana a gidajen Radio lakanin Gauta Club.

Kwamared Waiya ya kuma godewa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake kokari wajen hada kan yan Adawar jihar don yin siyasa ba da gababa da kuma kokarin ciyar da jihar Gaba.
Da yake jawabi shugaban kungiyar ta Gauta Club Alhaji Hamisu Dan Wawu Fagge yabawa kwamishinan yada labarai yayi bisa yadda yake tafiyar da aikinsa daga ciki hadda yadda aka tsaftace siyasar Baka a gidajen Radio, in da yace har makwaftan jihohi sun fara sha’awar su suna masu neman iznin kwaikwayon wannan tsari na Jihar kano.
Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai
Yayin karbar rantsuwar sabbin dattawan na Kungiyar Gauta daga jamiyyu daban daban sunyi Alkawarin rike gaskiya da Amana, da kuma bin doka da kaidah.
Daga nan sai wasu daga cikin su suka godewa kwamishinan yada labaran bisa yadda yake kokari wajen tsaftace adawar siyasa a jihar Kano.
Mutane goma sha hudu aka rantsar a matsayin kwamatin dattawan kungiyar ta Gauta Club, Wanda suka hadar da Alhaji Bashir Adamu Gaya, Idris Danzago, Alhaji Isah Bello Jaa, Alhaji Ibrahim Dan Adandan, Alhaji Damina Ali Gwarzo, Alhaji Auwalu Maiturare Bichi, Kwamred Rabiu Bala, Muhammad Idris Matashin Dan Fansho, Sauran sun hadar da Dan Jummai Gwaska, Injiya Dayani Tarauni, Lawan Sofi Danmasanin Gaya, Hajiya Binta Sayyadi, da Hajiya Habiba Dandalla, Sai kuma Hon. Aminu Bichi.