Kannywood: Hamisu Breaker ya Magantu kan batun gaskiyar soyayyarsa da jaruma Rakiyya Moussa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Shahararren mawakin nan Hamisu Breaker ya bayyana cewa babu wata soyayya tsakanin sa da jaruma Rakiyya Moussa yar asalin kasar Niger.

 

Idan za’a iya tunawa jarumar ta yi wata hira Inda tace tana fuskantar kalubale sosai akan soyayya saboda wanda take so yaki karbar soyayyarta, wanda hakan yasa ta cikin mawuyacin hali.

 

Mutane da yawa sun ta danganta maganar jarumar da cewa Hamisu Breaker ne wanda take magana akan sa, saboda kusancin da ke tsakanin su .

 

“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lfy dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan wata batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar Asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita wasu mutane na cewa wai dani tayi soyayya kuma har na juya mata baya Sam Sam wanna maganar ba haka take Hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai Mutunci”.

 

Mawakin dai ya bayyana hakan ne ta sashihin shafin sa na Facebook da yammacin wannan rana ta Asabar.

 

An dai jima ana ganin akwai soyayya tsakanin Rakiyya Moussa da mawaki Hamisu Breaker saboda yadda suke gudanar da aiyukan su musamman wakokinsa na video.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Kwamitin Majalisar Wakilai ya gabatar da shawarar kara Jihohi 31 a Nigeria

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Kwamitin majalisar wakilan Nigeria mai kula...

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...