INEC ta tanadi Kwararrun lauyoyin SAN guda tara domin kare sakamakon zabe

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Akalla Manyan Lauyoyin Najeriya 9 ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta tanada domin kare sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

 

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, Abubakar Mahmoud (SAN) ne zai jagoranci tawagar. Sauran mambobin sun hada da Stephen Adehi (SAN), Oluwakemi Pinheiro (SAN), Miannaya Essien (SAN), da Abdullahi Aliyu (SAN).

Kannywood: Hamisu Breaker ya Magantu kan batun gaskiyar soyayyarsa da jaruma Rakiyya Moussa

 

Rahotanni sun nuna cewa SAN hudu wadanda ma’aikatan sashen shari’a ne na INEC suma na daga cikin tawagar Kwararrun lauyoyin wadanda suka hadar da Garba Hassan, Musa Attah, da Patricia Obi.

 

INEC ta kashe sama da Naira Biliyan 3 don kare sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi na ranar 18 ga Maris.

Nasarar Abba Gida-gida ta wucin gadi ce – Ganduje

 

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ‘yan takara da dama da suka sha kaye a zabukan sun shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da na jihohi domin kalubalantar sakamakon zaben.

 

Ya zuwa yanzu dai an shigar da kararrakin zabe sama da 100 daga ‘yan takarar jam’iyyunsu a fadin kasar.

 

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da na am’iyyar Labour, Peter Obi, dana jam’iyyar Action Alliance, Solomon Okangbuan; da Allied Peoples Movement, Chichi Ojei, sun shigar da kara kan sakamakon zaben shugaban kasa.

 

A ranar 1 ga Maris, 2023, hukumar ta bayyana Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...