Daga Kamal Yakubu Ali
Babban Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kano akan sha’anin hotunan wato SSA Photography Aminu Dahiru ya tallafawa wasu dalibai su goma Sha biyar da kudaden da zasu biya kudin makarantun gaba da sakandire a kano.
Da yake mika tallafin naira dubu 20 ga kowanne daga cikin daliban Aminu Dahiru ya bukace su da su zamo masu Maida hankali wajen koyan abun da malaman su suke koya musu don inganta rayuwar su.
Yace ya basu tallafin ne domin suma su tsaya su yi karatun don suma a nan gaba su tallafawa kansu da yan uwansu dam ma sauran al’umma baki daya.
Ba zan biya duk wani bashi da Ganduje ya ciyo bayan zabe ba – Shawarar Abba Gida-gida ga bankuna
Wannan dai bashi ne karon farko ba, da Hadimin Gandujen yake tallafawa Matasa ta fannoni daban-daban musamman sha’anin Ilimi da Kuma sana’o’in dogaro da kai don inganta rayuwar matasa.
Aminu Dahiru ya alkawarin cigaba da tallafawa Matasa musamman a sha’anin Ilimi Inda yace ” idan ka taimaki mutum ya Sami ilimi babu shakka ba shi kadai ka taimaka ba, domin baka san iya kacin wadanda Ilimin zai amfana ba.