Daga Maryam Muhd Ibrahim
Kungiyar ma’aikatan Radio da talabijin da wasan kwaiwayo ta kasa reshen jihar kano ta taya sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaben gwamnan jihar kano.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na jihar kano Babangida Mamuda Biyamusu Kuma ya aikowa kadaura24.
Abba Gida-gida ya shawarci masu gine-gine a wararen Gwamnatin kano da su dakata
Sanarwar tace tana taya Abba Gida-gida Murnar a madadin kafafen yada labarai dake kano,tare da fatan zai samar da kyakyawar dangantaka tsakanin sa da kafafen yada labaran don samun nasarar gwamnatin sa.
Ina godiya ga yan jaridu bisa hadin kan da suka ba ni inji mai magana da yawun Ganduje Abba Anwar
” Babu Shakka kasancewar ka gwamnan jihar kano a wannan lokaci zai baiwa jihar damar amfana daga basira da kwarewar da kake da ita wadda ka nuna ta lokacin da ka rike kwamishinan aiyukan na jihar kano, lallai Kano zata sami cigaba ta fannoni daban-daban”. Inji sanarwar
Yace kungiyar taza yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta baiwa sabon zaɓaɓɓen gwamnan kano hadin kai da goyon baya don ganin ya Sami nasara a mulkin da zai yi was jihar kano.