Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jaddda goyon bayansa bisa tsarin e-naira da babban bakin Nigeria da babban bankin kasa CBN na E-Naira, ya bujiro dashi wanda yace zai taimaka wajen bunkasa harkokin Kasuwanci da cigaban kasa.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin daraktan CBN shiyar Kano Alhaji Muhd Hamisu Musa yayin da suka ziyarce shi a fadar sa.
Sarkin Kano ya taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaben gwamnan jihar
Cikin sanarwar da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Sarkin na Kano ya ce tsarin na E-naira zai tamakawa yankasuwa da sauran al’ummar kasar nan.
Sake duba sakamakon zaben gwamnan Kano, APC ta bukaci yan’yan ta su zauna lafiya
Aminu Ado Bayero ya kuma bukaci da babban bakin kasa da ya gyara matsalar network da ake samu yayin hada-hadar kudade, wanda a cewar sarkin yana kawo Nakasu da tarin kalubale da al’umma ke fuskanta.
A nasa jawabin babban daraktan bankin Alhaji Muhd Hamisu Musa ya ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin shaida masa irin hanyoyin da suke bi wajen wayar da kan alumma amfanin tsarin na E-naira da babban bakin kasa ya bujiro da shi domin taimakawa yan kasuwa.
A yayin ziyarar, daraktan na tare da dukkan shugabannin sassa na bankin shiyyar Kano.