Daga Rahama Umar Kwaru
Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf (wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida) na jam’iyyar NNPP ya ce matansa da ‘ya’yansa ba za su shiga sabgar mulkin da zai yi jihar kano ba.
Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen karbar takardar shaidar lashe zabe a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta ke kano.
INEC ta baiwa Abba Gida-gida Shaidar lashe zaben gwamnan Kano
Zababben gwamnan ya ce ba zai bari ‘yan uwansa su yi wani tasiri a harkokin mulkin sa a lokacin gwamnatin sa ba, saboda ba tare suka yi rantsuwar kama aiki da shi ba.
“Mata na ba za su shiga harkokin mulkina ba. ‘Ya’yana ba za su shiga cikin harkokin mulki ba. Kuma zan iya baku tabbacin cewa haka shima mataimakina.” inji shi.