Khadija Abdullahi Aliyu
Rundunar Yan Sandan ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mutane da ake zargi da cinna wuta a gidan mawaki Dauda Kahutu Rarara.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa.
Ku Karanta: Cikin kwanaki darin farko zan kyautata Ilimi a Kano – Abba Gida-gida
Yace sun cafke mutanen ne bisa zargin Kone wani bangare na gidan mawakin na Jamiyyar APC, biyo bayan samun Nasarar Abba Kabir Yusif na Jamiyyar NNPP a zaben Gwamnan Jihar Kano.
Ku Karanta: Dan takarar APC yayi watsi da sakamakon zaben gwamnan Bauchi
Yace za su gurfanar da dukkan Wanda aka samu da Hannu cikin lamarin da zarar sun kammala bincike.