Cikin kwanaki darin farko zan kyautata Ilimi a Kano – Abba Gida-gida

Date:

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, ya ce zai gudanar da gwamnatin da za ta fifita maslahar al’umma da kuma kyautata ilimi.

 

A jiya ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar da ranar asabar din da wuce.

 

A tattaunawarsa da BBC Abba Kabira ya ce al’umar jihar sun nuna masu ƙauna a lokacin da yake ya ƙin neman zaɓe da kuma a ranar zaɓe, kan haka ne ma ya ce bai yi mmaki ba da hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

 

Ya ƙara da cewa ba zai yi sako-sako wajen yaƙi da cin hanci da kyautata rayuwar al’umma ba.

 

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan na Kano ya ce zai bayar da fifiko wajen kyautata ilimi da lafiya da kasuwanci da tsaro da harkokin noma.

 

Abba Gida-gida ya ce cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa zai yi kokarin kyautata ɓangaren ilimin jihar.

 

Abba Gida-gida – wanda tsohon kwamishinan ayyukan ne zamanin mulkin tsohon gwaman jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso – ya alƙawarta cewa zai ƙarasa duk ayyukan da gwamnatin jihar ta yanzu ta faro matuƙar za su amfanar da al’ummar jihar.

 

Sabon gwamnan ya lashe zaɓen da aka gudanar da ƙuri’u miliyan 1,019,602, bayan doke babban abokin hamayyarsa mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya samu ƙuri’u 890,705.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...