Daga Halima Musa Sabaru
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta ce hankalinta ya kai kan wani katin shaida da aka buga da sunan hukumar a matsayin katin shaidar jami’an tsaro domin amfani da shi a ranar Asabar 18 ga watan Maris na shekarar 2023 da za’a gudanar da zaɓen gwamna da na yan majalisar dokokin jiha a Jihohin Nigeria.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin Ilimintarwa akan zaɓe, Barista Fesus Okeye, ya fitar yace katin shaidar ba daga gare su yake ba, domin kuma katin jami’an tsaro yana tare dasu, kuma duk mutumin da aka kama da makamancin wannan katin shaida mai dauke da suna da tambarin hukumar ta INEC, ba shakka za’a kama shi kuma doka za tayi aiki a kansa.
Yace a saboda haka hukumar take kira ga al’umma da su sanya idanu su lura sosai, su kuma kai tahoton duk wani abu mara tabbas ga hukumomin tsaro a yayin zaɓen.