Zargin kisa: IGP zai bada ladan miliyan 1 ga duk wanda ya kamo ɗan majalisar wakilai na Bauchi

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta bayyana cewa tana neman dan majalisar wakilai, Yakubu Shehu ruwa a jallo, tare da bada Naira miliyan 1 ga duk wanda ya kamo shi.

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ruwaito Shehu na wakiltar mazabar Bauchi ta tarayya a jam’iyyar PRP amma daga baya ya koma APC.

 

Wannan yana kunshe ne a cikin sanarwar ‘Yan Sanda ta Musamman CB: 2685/Bsx/VOL.T/4s wacce Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya raba a yau Talata a Bauchi.

Karanta: Zaben kano: Rundunar yan sanda ta sake turo sabon Kwamishina jihar kano

Sanarwar ta ce rundunar ƴansandan Nijeriya, karkashin ikon Sifeto-Janar, Usman Baba, ta bayyana mamban Yakubu Abdullahi Shehu da ake nema ruwa a jallo.

 

Ana neman sa “dangane da zargin hada baki, haddasa mummunan rauni, tada hankalin jama’a da kuma kisan kai.

 

“’Yan sanda na neman duk wanda ke da sahihin bayanin da zai kai ga kama shi domin yi masa tambayoyi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya kan zargin aikata laifuka.

 

“Duk wanda yake da bayanin da zai taimaka wajen kama shi to ya tuntubi lambar waya; 08151849417 ko kuma ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda mafi kusa”.

 

Ta ce hukumar tsaron ta bukaci duk wanda ke da bayanai masu amfani game da inda yake da ya tuntube ta, inda ta yi alkawarin ba dan majalisar kyautar N1m.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...