Iftila’in Gobara: Sarkin Kano ya jajantawa yan kasuwar Singer

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, JP, ya jajantawa “yan Kasuwar Singa dake cikin birnin Kano bisa iftila’in gobara data tashi a kasuwar.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun sakataren yada labarai na Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Naisa Wanda kuma ya rabawa manema labarai.

 

Sanarwar ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin ya nuna damuwarsa matuka a lokacin da ya samu labarin tashin gobarar.

 

Ku Karanta: Zaben kano: Rundunar yan sanda ta sake turo sabon Kwamishina jihar kano

Haka kuma Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake mika sakon jajantawa ga “yan Kasuwar Kurmi da Kasuwar Rimi bisa ifila’in Gobara da suka samu a kwanakin baya.

Ku Karanta: Zargin kisa: IGP zai bada ladan miliyan 1 ga duk wanda ya kamo ɗan majalisar wakilai na Bauchi

 

Sarkin ya jajantawa da nuna alhini, inda yayi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.

 

 

Yayi kira kira ga yankasuwar da kungiyoyin yan Kasuwa su cigaba da yawaita adduo’oi da kuma daukar dukkan matakan kare kiyaye afkuwar irin wannan iftila’I a koda yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...