Daga Rukayya Abdullahi Maida
A ranar Talatar nan ne gobara ta kone injinan cirar kudi na ATM har guda uku na bankin Zenith dake kan titin Tafawa Balewa a karamar hukumar Nasarawa dake jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta kano ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Talata a Kano.
Ku Karanta: Zaɓen Kano: Za a baza jami’an ’yan Sanda 18,748 Saboda Zaben Gwamna
Abdullahi ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran waya da misalin karfe 12:06 na rana. daga wani Ghali Muhammad cewa gobara ta tashi a wuraren cirar kudin na injinan ATM.
Zaben kano: Rundunar yan sanda ta sake turo sabon Kwamishina jihar kano
“Da samun labarin, mun yi gaggawar tur jami’an mu da motocin kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 12:11 na rana, domin kashe gobarar domin kada ta shafi sauran na’urorin ATM din ,” inji shi.
Abdullahi ya kara da cewa, gobarar ta kone na’urorin ATM guda uku gaba daya, yayin da sauran ukun suka kone kadan.
Ya alakanta lamarin da tartsatsin wutar lantarki daga injinan na ATM.