Daga Halima Musa Sabaru
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya jajanta wa wadanda gobara ta shafa a kasuwannin Kano na Kurmi, Rimi da kuma mawakin kwanan nan.
Yayin da yake yi musu addu’ar samun karfin gwiwa don jure wannan rashi ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa, ya bukace su da su rika lura da kuma kashe kayan wutar lantarki idan zasu tashi daga wuraren kasuwancinsu.
Ku Karanta: Zaben kano: Rundunar yan sanda ta sake turo sabon Kwamishina jihar kano
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina mika sakon jajantawa ga duk wadanda suka yi hasarar dukiyarsu, da fatan Allah ya kiyaye gaba,” inji shi.
Ku Karanta: Zargin kisa: IGP zai bada ladan miliyan 1 ga duk wanda ya kamo ɗan majalisar wakilai na Bauchi
“Wannan musiba ba ta wadanda shagunansu suka kone ba ne kadai, abu ne da ya shafi al’ummar kasar nan baki daya, Allah Ya ba su kwarin guiwa su dauki wannan a matsayin iftila’i daga Allah,” Ya yi addu’a.