Daga Rahama Umar Kwaru
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana cewa yana da kyakyawar dangantaka da dakkanin gwamnonin da ya yi aiki da su a kano .
A cewarsa…“Ina da kyakkyawar alaka da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran tsofaffin Gwamnonin da na yi aiki da su a gwamnatocin baya a matsayin da Shekarau da nayi aiki da shi a matsayin shugaban karamar hukuma, da kuma Kwankwaso da nayi masa kwamishina da kuma a yanzu a matsayina na Mataimakin Gwamna Ganduje, duk kuwa da bambancin jam’iyyar siyasa.
Gawuna ya bayyana hakan ne yayin da ya tattaunawa da shi a cikin wani shiri na gidan talabijin din TVC mai suna “Countdown Nigeria Decides 2023″.
Ya kuma kara da cewa bai yarda a samu gaba ko hatsaniya tsakanin yan Siyasa a Kano ba , kawai kamata yayi mufi fifita jihar kano fiye da son kanmu”.
Ban ce a zabi wani dan takarar gwamnan kano da ba Abba Gida-gida ba – Sen. Kawu Sumaila
A cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24, yace dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya bukaci al’ummar Kano da su yi la’akari da kwarewa da amincin ‘yan takara a matsayin ma’auni yayin kada kuri’a.
“Ina da kwarewar da ake bukata a harkokin mulki wanda ya sanya ni a saman duk sauran ‘yan takarar gwamna” Gawuna ya bayyana”.
Ya kuma nanata bayar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomin jihar idan aka zabe shi a matsayin Gwamnan kano.