Takarar Kwankwaso: Kaddara Ko Ganganci?
Yadda wasu kananan hukumomi suka tafka babbar asara sanadin takarar Kwankwaso
Ra’ayin Aminu Dahiru
Lokaci ya yi da yakamata al’ummar jihar Kano su tambayi kansu shin takarar shugabanci kasa da tsohon gwamna Dr Rabiu Musa Kwankwaso yai kaddara ce ko kuma ganaganci?
Irin wannan dalili ne yasa masana kan jan kunnan duk wata al’umma da tai karatun-ta-nutsu kafin daukar kowane irin mataki musamman kan abubuwanda kan iya shafar rayuwarsu ta kowane fanni.
Da farko dai shi kwankwaso yan san takararsa ba wata aba bace face san-sarai dan yasan takarar gangan yai amma haka yai ta tunzura matasa zu zabeshi duk da ya san ba zai kai labara ba, ko kuma nace babu shi a lissafi. Amma zabe ya nuna kowa matsayinsa. Daga karshe dai iya jiha daya ya samu a cikin jihohi 36 da birnin tarayya. Kaga wanda zai koyi darasi wannan shi ne lokacin da ya dace.
Koma dai menene wannan takara ta gangan da Kwankwaso ya yi ta jawowa al’ummar jihar kano asara kala-kala, duba da yadda wasu jajirtattun ‘yan majalisun tarayya su ka rasa kujerinsu.

Ba yanzu al’ummar kananan hukumomin kamar irinsu Nassarawa, Dawakin Kudu da Warawa da Tarauni da Fagge da Gwale da Dala da sauransu za su gane irin illa da wannan takarar gangan ta jawo musu ba sai ranar da su ka farka daga baccin da su ke yi sabbin wakilai su ka kama aiki.

Zakakuran wakilai irin su Hon. Nasir Ali Ahmed mai wakiktar Nassarawa da Hon. Mustapha Bala mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa da Hon. Hafizu M. Kawu mai wakiltar Tarauni da Hon. Aminu Goro mai wakiltar Fagge da Hon Abdullahi Ken-Ken dake wakiltar Gwale da Hon. Babangida Alasan Yakudima mai wakiltar Dala duk sun rasa kujerinsu duk da irin bauta da wakilci nagari da suka yiwa al’ummominsu.

Kamar yadda kowa ya san yadda wadannan wakilai suka sadaukar da rayuwar su wajen samar da ayyukan yi, sun gina makarantu, sun gina titina sun bada tallafin karatu, sun gina filayan wasa kuma sun mika kudurai kala-kala dan ganin gwamnatin tarayya ta kyautatawa al’umominsu.

Haka zalika wadanda aka zaba saboda san rai su maye gurbin wadannan jajirtattun ‘yan majalisu ba su da gogewa ta aiki sannan wanda ya basu wannan takara ya dorasu ne dan su zama saniyar tatsa ba dan su kyautawa al’ummomin da za su wakilta ba. Kamar dai yanda ya dace da kudurin kwankwasiyya na kassara wannan jiha da gurbata tunanin matasa.

Hakika takarar da kwankwaso yai ganganci ne da ya illata wasu daga cikin kananan hukumomin Jihar Kano hakan kuma zai bayyana a fili lokacin da wakilai masu ci suka bar ofis, sabbi suka kama aiki.