Ban ce a zabi wani dan takarar gwamnan kano da ba Abba Gida-gida ba – Sen. Kawu Sumaila

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Zababben sanatan Kano ta Kudu, Hon. Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana marawa wata jam’iyya baya a zaben gwamna da ke tafe.

 

Kadaura24 ta rawaito Mataimaki na musamman ga Sanata Sumaila kan sabgar yada labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano.

 

Abbas yace wannan labari ba shi da tushe ballantana makama.

Da dumi-dumi: Ganduje da Shekarau sun gana a mundubawa gidan Sardaunan Kano

 

Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yada wannan labari na bogi, inda yace a shirye su ke su dauki matakin shari’a kan duk mutumin da ke neman bata sunan Hon. Suleiman Abdul Rahman Kawu Sumaila

 

Zaɓen Kano: Kwamitin Zaman lafiya na Kano ya gana da Kwankwaso da Abba Gida-gida

Yace Sanata Kawu Sumaila cikakken mai biyayya ne ga jam’iyyar NNPP da jagoranta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a don haka ba zai taba furta kalaman da ke nuni da a zabi wata jam’iyya ta daban ba a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

 

Abbas ya rawaito Sanata Kawu Sumaila na kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano tare da sauran ‘yan takarar majalisar jiha a tutar jam’iyyar NNPP a zaben da zai gudana a ranar 18 ga watan Maris.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...