Bai dace a rika korar matan da suka yi ciki a makarantu – inji Ministar Mata

Date:

Daga Hadiza Ahmad Mai Gari

 

Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta shawarci ministar mai jiran gado ta ma’aikatar da kada ta bari a riƙa korar ɗalibai da su ka yi ciki daga makaranta.

 

Ta ce ilimi shi ne ginshikin rayuwar ƴaƴa mata.

Tallen ta ba da wannan shawarar ne a wajen wani taron tattaunawa da ma’aikatar harkokin mata ta tarayya ta shirya ranar Juma’a a birnin New York.

 

Ta ce babu wata yarinya da za a bari a baya in dai Nijeriya na son cimma burin buƙata ta 5 a muradun ci gaba mai dorewa, kan daidaiton jinsi da kuma karfafa dukkan mata da ‘yan mata nan da shekarar 2030.

 

“Karfafa tattalin arziki ilimi; ba kawai ilimin yarinyar ba, har ma da damar ilimi na biyu ga yara mata da suka yi ciki yayin da suke makaranta.

 

“sai a kore su daga makaranta a bar mai laifi (wanda yai cikin). Ba ta yi ciki ita kaɗai ba amma wanda ya yi mata ciki za a bar shi a makaranta ita kuma a kore ta.

 

“Babu wata yarinya da za a kora daga makaranta saboda tana da ciki. Idan an kore ta daga makaranta, shi ma a sallame yaron da yai mata cikin daga makaranta.

“Ya kamata a bar ta ta dawo bayan ta haifi jaririn kuma ta ci gaba da karatunta,” in ji ministar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...