Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na taya zababben shugaban kasa Sen.Bola Ahmed Tinubu da mataimakin zababben shugaban kasa Sen.Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023.
“Ni da kaina da abokin takara ta Hon.Murtala Sule Garo muna muku fatan alkhairi da wannan nauyi da Allah ya dora muku, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara muku hikima, kwarin gwiwar aiyukan da zasu kara inganta Nigeria”.
“Jagaban, kai ne mutumin da ya dace a halin yanzu, nasararka nasara ce ga dimokuradiyya, ka yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyarmu ta APC.”
“Ka tabbatar da cewa kai dan dimokradiyya ne na gaskiya wanda ya nuna jajircewa, kishi da sadaukarwa don ci gaban kasarmu.”
“Mun gode muku bisa jajircewarku da tsayin dakanku domin mun yi imanin cewa kuna da kyakkyawar niyya don cika alkawuran da kuka yi a lokacin yakin neman zabe”.
A sanarwar da babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24,ya ce Gawuna ya kuma mika godiyarsa ga al’ummar jihar Kano bisa zaben jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.