Ahmad Lawan ya sake lashe zaben Sanatan Yobe-ta-Arewa

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya lashe zaben Sanatan Yobe-ta-Arewa a Yobe.

 

Da ya ke bayyana sakamakon zaben a Gashua a yau Litinin, jami’in zaben, Farfesa Omolala Aduoju na jami’ar tarayya, Gashua, ya ce Lawan ya samu kuri’u dubu 91,318.

 

“Bayan cika sharuddan doka kuma ya samu mafi yawan kuri’u, an bayyana Alhaji Ahmed Lawan na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kuma aka dawo zabe,” inji shi.

 

Ya ce babban abokin hamayyar Lawan, Sheriff Abdullahi, na jam’iyyar PDP, ya zo na biyu da kuri’u 22,849, yayin da ɗan takarar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Garba Umar, ya samu kuri’u 7,210.

 

Mista Aduoju ya ce jam’iyyar Action Democratic Party, ADP ta samu kuri’u uku duk da cewa jam’iyyar ba ta tsayar da dan takara a zaben ba.

 

“Jimillar kuri’un da aka kada a zaben sun kai dubu 126,677 daga cikinsu 122,136 sun yi aiki kuma an ki kuri’u 4,541,” inji shi.

 

Gundumar ta ƙunshi kananan hukumomin Machina, Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko da Yusufari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Adam A Zango ya sake Aurar Jarumar Kannywood

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A....

NNPP ta yi watsi da sakamakon Zaben Ghari da Tsanyawa a Kano

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta ƙi amincewa da...

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano

Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan...