Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar bashi da inganci don haka akwai bukatar dole soke shi.
Obasanjo ya roki shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Najeriya daga cikin hadarin da take neman fadawa .
A cikin sanarwar da Obasanjo ya fitar ya ce ba wani boyayyen abu ba ne yadda jami’an INEC a rumfunan zabe sun gaza yin amfani da na’urar da aka tanadar musu, wanda hakan tasa ake zargin sun yi aringizon kuri’u.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Janairu, Obasanjo ya fito fili ya amince zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a wannan zaben da aka gudanar.