Zaben Shugaban Kasa: Kwankwaso ya doke Tinubu da Atiku a Kano

Date:

Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa

 

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya Sami kuri’u mafi rinjaye a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a jihar Kano.

 

Babban jami’in tattara sakamakon zabe Shugaban kasa a Kano Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan karbar sakamakon Zaɓen daga kananan hukumomin 44 dake jihar kano.

 

Farfesa Bilbis yace Kwankwaso ya Sami kuri’u 997279 yayin da abokin takarar sa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zo na biyu da kuri’u 517341sai Kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP na ya ke biye masa da kuri’u 131716.

 

Babban jami’in tattara sakamakon Zaɓen ya bayyana sakamakon Zaɓen Shugaban kasa na kano ne a gaban wakilan jam’iyyu da masu Sanya idanu na gida dana waje da jami’an tsaro da kuma yan jaridu.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an gudanar da zaben Shugaban kasa dana yan majalisun tarayya a ranar asabar 25 ga watan fabarairun 2023.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...