Wasu Fusatattu Matasa sun bankawa ofishin INEC na Takai Wuta

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Rahotanni daga karamar hukumar Takai na nuna cewa wasu fusatattu sun bankawa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke karamar hukumar Takai ta wuta inda ta kone kurmus.

 Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 09:30 na safe, inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka fara lakada wa mutane duka, lamarin da ya tilastawa masu sa ido kan zabe da ‘yan jarida da jami’an hukumar zabe ta INEC gudu domin tsira da rayukansu, amma ‘yan bangar sun kona ofishin.
Jaridar Globaltraker ta rawaito daya daga cikin wadanda abin ya shafa kuma dan jarida daga yankin Sale Nasko ya ce ana kyautata zaton wasu fusatattu matasane da suke ganin baza su yi nasara ba suka aika wannan mummunan aikin.
 Wani wanda lamarin ya rutsa da shi kuma a halin yanzu yana kwance a asibiti da raunuka daban-daban ya ce an kama wadanda ake zargi da kai harin kamar Garba Gambo, Shehu Na-marka, Abdullahi Dan-jalingo da kuma wanda ba a san ko wanene ba.
 Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da jami’in tattara sakamakon zabe na karamar hukumar ke jiran isowar mazabu biyu na karshe (Takai da Kachako) kafin ya bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jiya.
 Ya ce wasu sojoji ne suka ceto su.
 “Mun sahimci cewa harin bai shafi sakamakon zaben ba”, in ji wanda abin ya shafa.
 Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Adam A Zango ya sake Aurar Jarumar Kannywood

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A....

NNPP ta yi watsi da sakamakon Zaben Ghari da Tsanyawa a Kano

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta ƙi amincewa da...

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano

Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan...