Zaben2023: ICPC ta cafke masu sayen ƙuri’u a jihohi biyar

Date:

Hukumar ICPC mai binciken laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta kama mutum tara saboda laifin sayen ƙuri’u a jihohi biyar na Najeriya.

 

ICPC ta kama mutanen ne lokacin gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a jihohin Osun da Ondo da Borno da Akwa Ibom da Sokoto.

 

A cewar hukumar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Tuwita, an kama mutum huɗu masu sayen ƙuri’u a jihar Osun, biyu a jihar Sokoto sai kamen da ICPC ta yi a Ondo da Akwa Ibom da Borno inda aka kama mutum ɗaya kowace jiha.

 

Zuwa yanzu dai hukumar ta ce mutanen da aka kama a Osun na tsare a ofishinta da ke jihar kuma an same su ne da wasu takardu ɗauke da sunaye da kuma lambobin wayoyinsu har da bayanan asusun ajiyar bankinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...