Zaben Shugaban Kasa: NNPP A Kano ta fitar da sanarwa ta musamman

Date:

 

 

Sanarwa ta Musamman

 

Bayanan sirrin da muka samu sun tabbatar da cewa gwamnatin jahar Kano da jam’iyyar APCmaimulki sun tanadi ‘yan daba a wurare daban daban da niyyar tada tarzoma bisa ganin alamun nasarar jam’iyyar mu ta NNPP a zaben da ya gudana yau Asabar.

 

A saboda haka, muke kira ga hukumomin tsaro da su kara zage damtse wajen kare lafiyar ma’aikatan zabe, masu sa idanu akan zabe da wakilan jam’iyyu da kuma al’ummar jahar Kano baki daya.

 

A bisa wannan dalili, muna shawartar dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP da su tsaya tsayin daka don tabbatar an kidaya dukkanin kuri’un da aka kada tare shigar da sakamako cikin na’urar da hukumar zabe ta tanadar sannan kuma a tabbatar ta an bayyana sakamakon kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanadar.

 

Sanusi Bature Dawakin Tofa

Maimagana da Yawun Kwamatin Yakin Neman Zabe na Jam’iyyar NNPP Reshen Jahar Kano a Shekara ta 2023

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...