Daga Rukayya Abdullahi Maida
Amb. (Dr) Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya hori matasa da su rika haɗa kai wajen tafiyar da sana’o’in hannu domin amfanar juna da Kuma dorewar sana’ar ta su.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne ya da yake jawabi a wajen taron yaye wasu matasa maza da mata sama da guda goma wadanda ya dauki nauyin koya musu sana’o’in kwalliya da girke-girke.
Amb . Yunusa Yusuf yace matukar matasan da suka koyi sana’a irin daya zasu haɗa kansu wajen tafiyar da sana’ar to babu shakka zasu jima suna morar sana’ar , Kuma hakan zai kara musu dankon zumunci.
” Idan kuka hadu to zaku taimaki junankun, a cikin ku Wani yafi Wani iya abun da koka koya, Wani Kuma yasan jama’a don haka idan kuka hadu sai ku Samar da wata ma’aikata wacce Kuma zaku iya daukar ma’aikata Kuma ku taimakawa kanku wajen ginawa kanku arzikin Mai yawa”. Inji (Dr) Yunusa Yusuf Hamza
Falakin Shinkafin wanda shi ne Jarman matasan arewa ya ce aikin tare da juna bazai yiwuwa ba , dole sai Kuma zama Kuna da amana domin daga lokacin da wani ya fara yunkurin cutar abokin sana’arsa to da wancan ya gano shi kenan tafiyar zata watse, don haka ku rike gaskiya da amana.
Kimanin matasan sama da goma ne suka koyi sana’o’in dogaro da kai na kwalliya da girke-girke wanda suka kwashe kimanin watanni biyu suna koya.