Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar NNPP a mazaɓar Wudil da Garko a jihar Kano, Kamilu Ado Isa ya rasu.
Ya rasu ne a jiya Lahadi bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2023/02/IMG-20230219-WA0008-191x300.jpg)
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda kafin babban zaɓen Najeriya na 2023.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2023/02/IMG-20230108-WA0000-1-300x225.jpg)
Ado Isa ya kasance tsohon mataimakin kontrola-janar na hukumar tsaron farin kaya na Civil Defence.
NNPP dai na cikin manyan jam’iyyun siyasa da ake hasashen za su iya taka rawar gani a zaɓen da ke tafe.