Yan jam’iyyar PDP  sama da 10,000 ne suka sauya sheka zuwa NNPP a Kano

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria
 Kwanaki shida kafin gudanar da babban zaben kasa, shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Kano sun koma jam’iyyar NNPP .
 A wani gagarumin gangami da aka gudanar, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali tare da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Bishop Isaac Idahosa ne suka tarbi wadanda suka sauya shekar a Kano .
Talla
 Shugabannin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Shehu Wada Sagagi sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne, sakamakon rashin tafiyar da tsarin dimokuradiyya a cikin jam’iyyar da kuma son zuciya da shugabannin jam’iyyar na kasa suke yi.
Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil
 Da yake jawabi a wajen taron, Shehu Sagagi ya ce shi kan sa tare da shugabannin kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP na jihar Kano su 36, shugabannin kananan hukumomi sama da 700, shugabannin mazabu sama da 8,000, wakilan jam’iyyar na kasa 44 da kuma wakilan mazabu 1,452 ne suka shiga jam’iyyar NNPP.
 “Siyasa magance ta yawa , muna kyautata zaton Sen. Rabiu Musa Kwankwaso zai kai mu ga nasara tun daga matakin kasa har jiha” in ji Sagagi.
 Ya kuma zargi jam’iyyar PDP da yiwa kanta zagon kasa a jihohi kamar Kano ta hanyar barin irin su Sanata Kwankwaso su fice daga jam’iyyar duk da dimbin mabiyansu ba a jihar kadai ba har ma da kasa baki daya.
 A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben NNPP a jihar Kano, ya an bato shugaban NNPP na kasa yana taya sabbin wadanda suka sauya sheka murnar shiga jam’iyyar NNPP.
 A martanin da ya yi, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Bishop Isaac Idahosa ya tarbi wadanda suka sauya shekar cikin farin ciki, yana mai cewa da wannan gaggarumin sauya sheka mai cike da tarihi, NNPP za ta yi nasara a zabe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...