Ku zabi Tinubu, Ina fatan zai dora daga inda na tsaya – Buhari ya bukaci yan Nigeria

Date:

Daga Auwalu Alhassan Kademi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Nigeria da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC wato Asiwaju Bola Ahmad Tinubu saboda kishin kasa da yake da shi , sannan Kuma zai dora daga inda ya tsaya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon bidiyo da fadar shugaban kasa ta saki a yammacin wannan rana ta lahadi.
Talla
” Ni bana takara a wannan karon, amma jam’iyyar ta ta APC ta tsayar da dan takarar wato Bola Tinubu, wanda na sha fada cewa mutum ne mai kishin kasa cikakken dan Nigeria Kuma Ina fatan idan Allah ya so idan aka zabe shi zai dora daga inda na tsaya”. Inji Buhari
Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil
Shugaba Buhari ya kuma bukaci yan Nigeria da su sami nutsuwa su fito zabe a ranar zabe, sakamakon gwamnatin tarayya ta yi Shirin da ya dace don ganin anyi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wasu daga cikin jiga-jigan tafiyar Bola Tinubu sun jima suna zargin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yiwa takarar Tinubun zagon kasa, ta hanyar aiwatar da Sabon tsarin sauyin fasalin kuɗi da babban bankin Nigeria ya fito da shi .
Shugaba Buhari ya kuma baiwa yan Nigeria Hakuri sakamakon matsananci halin da suke ciki a dalilin wasu tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta fito da su, Inda yace an fito da tsarin ne don cigaban kasa ba don a musgunawa Wani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...