Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam Hon. Kabiru Dan Hassan ya yayi alkawarin cigaba da bada gudunmawar da ta dace don ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkanin matakai.
” Ni da Babana Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso Muna da kyakyawan dangantaka, dama wasu yan zuga ne suka so shiga tsakanin mu, kuma Allah ya basu Kunya, don haka nake baku tabbacin zan cigaba da yin duk mai yiwuwa don ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkanin matakai”. Inji Dan Hassan
Dan majalisar ya bayyana hakan ne lokacin da yake mika mukullan motoci guda 11 ga wasu yan jam’iyyar APC daga kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam.
Talla
Yace ya bada motocin ne saboda wadanda suka ci gajiyar tallafin su sami kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa jam’iyyar APC don ganin Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya lashe zaben dan majalisar tarayya da zai wakilci al’ummar kura madobi da garun.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
” Ina kira ga dukkanin magoya bayana da sauran yan jam’iyyar mu ta APC a kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam da su Kara kaimi Wajen shiga lungu da sako na kananan hukumomin don samun nasarar yan takarar mu na APC tun daga sama har kasa.
” Mai girma Dan takarar mu na majalisar wakilai Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya motoci nan guda goma Sha daya da zamu rabawa yan jam’iyyar APC , yau dai Ina ganin gutsiri tsuma ta kare a kananan hukumomin kura madobi da garun, yau Ina ga Zaman mu na biyu kenan tare da ni da Dr Musa Iliyasu Kwankwaso abun da nake so da ku shi ne duk cikinmu ba Wani dan wata jam’iyyar don haka mu haɗa kai don ganin mun yi nasara a zabe mai zuwa.