Daga Isa Ahmad Getso
Dan takarar majalisar tarayya a karamar hukumar Nasarawa a jam’iyyar PRP Hon. Ahmad Muhammad Sale ( Ahmad kaka) ya yi alkawarin samawa matasa dubu 50 aiyukan yi idan aka zabe shi .
Ahmad kaka ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da wani shiri na musamman a Gidan Radio Nigeria Pyramid FM Kano.

Yace yana da tsarin ganin dukkanin masana’antun dake karamar hukumar Nasarawa wadanda suka durkushe sun dawo aikin domin daukar matasan karamar hukumar Nasarawa aiyukan yi.

” Idan Allah ya taimake mu masana’antun da muke da su a karamar hukumar Nasarawa suka dawo aiki, an tsaya tsayin dake wajen ganin sun ɗauki yan asalin Karamar hukumar aiki, wanda zaka zai sa a rage masu zaman kashe wanda, tare kuma da bada dama ga masu abinchin da sauran kayan saye da sayarwa”. Inji Ahmad kaka
Ahmad Kaka ya kuma bada tabbacin idan al’ummar karamar hukumar Nasarawa suka zabe shi zai inganta harkokin ilimin saboda sai da Ilimi ne dan Adam yake sanin kansa, da Kuma gujewa duk wani abu da zai taimaki rayuwar su.
” Zamu baiwa matan karamar hukumar Nasarawa dama ta hanyar koya musu sana’o’in da kuma basu jari, don inganta harkokinsu da kuma tattalin arzikin Nasarawa da Kano dama kasa baki daya.