Daga Abubakar Sale Yakubu
Babbar Jami’ar dake kula da Shirin mata masu noman tsirarai domin samar da Magani ta Jihar Kano karkashin Ma’aikatar lafiya ta kasa da sashin dake lura da Maganungunan Gargajiya TCAM, TMP Hajiya Fanna Muhammad Kuwa, hadin guiwa da Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, sun shirya taron wayar da kai na yini guda, kan yadda mata da matasa za su yi noman tsirarai a Jihar Kano, tare da nuna goyon bayansu ga Dantakarar Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da mataimakinsa Hon.Murtala Sule Garo, bisa alkawarin tallafawa masu sana’ar noman tsirrai domin samar da magani da yayi, idan aka zabe shi a shekarar 2023.
Taron ya wanda aka gudanar da shi a babban dakin taro dake gidan Gwamnatin Kano.

Yayin taron wayar da kan an koyar da matasa maza da mata yadda zasu yi noma itatuwa na magani da sayar dasu, inda akalla mambobin TCAM, dubu uku ne daga Kananan hukumomin jihar Kano 44, suka halarci taron.
Cikin muhimman mutanen da suka Sanya albarka a wajen taron sun hadar da wakilin Ministan Lafiya da kungiyoyin fararen hula da mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan Maganungunan Gargajiya da Matar mataimakin Gwamnan Kano da dai sauransu.

Manufar Shirya taron wayar da kan ita ce, zaburar da Mata da matasa su shiga a dama dasu wajen noman tsirrai dan samar da magani a jihar Kano, an nunawa mahalarta taron barazanar dake samun tsirrai sabo da yadda ake sare bishiyoyi da dazuzzuka, wanda hakan ya shafi sannannun magunguna da ake da su.
Wakiliyar Minsitan Lafiya Pharm.Zainab Ujudu Shareef, wadda ita ce shugabar sashin dake kula da magungunan gargajiya a Ma’aikatar lafiya ta gabatar TCAM, tayi bayanin irin yadda mahalarta taron zasu yi amfani da basirarsu wajen samu kudin shiga idan suka rungumi noman tsirarai domin samar da Magani.

Cikin Wanda suka gabatar da makala a wajen taron akwai Farfesa Halima Muhammad Isa, daga sashin nazarin Tsirarai a tsagayar Aikin gona a Jami’ar Bayero ta Kano da Dr. Usman K-Formula, Wanda yayi jawabi kan alfanun dake tattare tsirarran dake samar da Magani da ke kewaye damu.
haka kuma Malam Nazifi Umar dake sashin nazarin kasa, a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Jihar Kano, yayi bayani kan taswirar kasa, da Kuma goyon bayan noman tsirarai dake samar da Magani masu yawa.
Da ta ke nata Jawabin Jami’ar dake kula da shirin mata da matasa masu noman tsirrai samar da magani ta jihar Kano, wadda ke karkashin kulawar sashin dake kula da magungunan gargajiya a Ma’aikatar lafiya ta kasa, TMP Hajiya Fanna Muhd Kawu Sarauniya, wadda ita ce ta shirya taron, ta baiwa dimbin mahalarta taron mata da matasa tabbacin cewa, wannan noman tsirrai domin samar da Magani zai fitar dasu daga cikin yanayin talauci cikin kankanin lokaci.
Ta Kuma bayar da tabbacin cewa matukar suka zabi Mataimakin Gwamnan Kano Dantakarar Jam’iyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna zai tallafa musu ta Ofishin Daraktan TCAM, Pharm.Zainab Ujudu Shareef, sabo da Gawuna ya kulla yarjejeniya cewar zai baiwa bangaren noman tsirrai domin samar da Magani kulawar data dace matukar aka zabe shi Gwamnan Kano.