Daga Abdulrashid B Imam
Dan takarar gwamnan jihar kano na jam’iyyar Labour Party, LP , Bashir I Bashir, ya fice daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Dan takarar gwamnan ya kaurace wa taron gangamin yakin neman zaben jam’iyyar a Kano tare da shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Mohammed Zarewa; kodinetan yakin neman zaben Peter Obi na jiha, Balarabe Wakili da; dan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Idris Dambazau.

Wata majiya da ke kusa da dan takarar ta tabbatar da sauya shekar Bashir da wasu jiga-jigan jam’iyyar LP zuwa APC a ranar Lahadin nan, inda ta ce babban dalilin da ya sa suka sauya shekar shi ne ana ware manyan masu ruwa da tsaki a Arewa wajen yanke shawara da kuma rashin samun cikakkiyar alkibla kan maslahar Arewacin Najeriya. .

Rahotannin sun tabbatar da cewa Bashir I Bashir ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Legas da Abuja inda suka amince da sharuddan sauya shekarsa.
Wata majiya ta rawaito cewa dan takarar jam’iyyar na LP ya amince da shi da magoya bayan sa zasu goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.