An yanke wa sojojin DR Kongo bakwai hukuncin kisa saboda ‘tsorata a gaban abokan gaba’ lamarin da ya sa suka gudu, a fagen daga da suke fafatawa da ‘yan tawayen M23.
Lamarin da kuma ya haifar tsoro da razani a zukatan al’ummar yankin.
Ranar Alhamis ne sojojin suka wuce ta tsakiyar garin Sake, kilomita 25 yamma da garin Goma da ke gabashin ƙasar .

”Suna ta harbi a iska bayan da suka guje wa abokan gaba a fagen daga”, kamar yadda mai shigar da ƙara a kotun sojin ƙasar ya bayana wa kotu ranar Asabar.

Hukumomi a lardin Kivu sun ce sojojin masu muƙamin Kofur sun musanta zargin, kuma lauyansu ya ce za su ɗaukaka ƙara game da hukuncin.
Mai gabatar da ƙarar ya zarge su da janyo kisan kai, bayan da fararen hula biyu suka mutu wasu huɗu kuma suka samu munanan raunuka, saboda razanarwar da sojojin suka janyo wa mutane.
A baya-bayan nan dai dubban mutane ne suka tsere wa muhallansu a garuruwan Goma da Minova yayin da ‘yan tawayen M23 ke ci gaba kusantar garuruwan daga garin Masisi da ke yammaci.
A watan Nuwamban bara, kotun sojin ƙasar ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin kisa saboda ”guduwa a filin daga” a lokacin faɗa da ‘yan tawayen, lamarin da ya haifar da tsoro da razana da kuma tarwatsewar fararen hula.
A DR Kongo ana yanke hukuncin kisa, to sai dai rabon da a zartar da hukuncin tun shekarar 2003, a maimakon haka ana sassauta hukuncin zuwa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.