Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya ce zaben 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.
Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja lokacin da yake amsa tambayoyinb manema labarai, bayan ya yi wa Majalisar Zartarwa ta kasa, bayani kan matakin shirye-shiryen gudanar da zaben.
Ya bayyana karancin man fetur da sake fasalin kudin Naira a matsayin manyan kalubalen da ke fuskantar INEC, ya ce duk da haka sun riga sun sami mafita akan haka .

“Mun sanar da ‘yan majalisar zartarwar dukkan shirye-shiryen da muka yi na gudanar da zabukan da kuma ‘yan kalubalen da muke fuskanta da kuma matakan da muka dauka domin magance su.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa: “Don haka, mun fito da wadannan kalubale kuma mun samo hanyoyin magance wadannan kalubalen don haka muna bada tabbacin zamu gudanar da zaben kamar yadda aka tsara; a ranar 25 ga Fabrairu don zaben kasa da kuma ranar 11 ga Maris don zaben Jiha.”
Shugaban na INEC ya kuma ce akwai shirin yiwa majalisar zartarwar bayani a ranar 10 ga watan Fabrairu.