Girgizar kasa: An ceto jaririya sabuwar haihuwa daga baraguzan gini

Date:

Masu aikin agaji sun ceto wata jaririya sabuwar haihuwa daga cikin baraguzan gine-ginen da suka rushe a sakamakon girgizar kasa a yankin arewa maso yammacin Syria ranar Litinin.

mahaifiyarta ta fara nakuda ne jim kadan bayan girgizar kasar, sannan ta haihu kafin ta rasu, in ji wani danginsu.
Majiyar ta ce mahaifin yarinyar da ‘yan uwanta hudu da kuma kanwar mahaifiyarta duk sun rasu a girgizar kasar.
An wani hoton bidiyo mai cike da mamaki an ga wani mutum na rike da jaririyar wadda ta yi budu-budu da kura, bayan da aka fito da ita daga cikin buraguzai a garin Jindayris.
Wani likita a wani asibiti na kusa da garin da aka ceto ta, Afrin ya ce jaririyar a yanzu tana nan cikin kyakkyawan yanayi.
Gidan da mahaifanta suke na daya daga cikin gine-gine 50 da rahotanni suka ce girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta lalata a Jindayris, wanda gari ne da ke hannun ‘yan hamayya a lardin Idlib da ke kusa da iyaka da Turkiyya.
Talla
Kawun jaririyar, Khalil al-Suwadi, ya ce suna samun labarin rugujewar ginin sai suka ruga domin su ga abin da ya faru.
”Mun ji murya a lokacin da muke tona buraguzai, ” kamar yadda ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
”Da muka kawar da kasar sai muka samu jaririyar da mabiyiyarta, sai muka yanke mabiyiyar aka tafi da jaririyar asibiti.”
Likitan yara Hani Maarouf ya ce an kai jaririyar asibitinsa a yanayi maras kyau, saboda ta kukkuje ga kuma tsananin sanyi da ya taba ta”.
”To amma yanzu ta samu sauki,” in ji likitan.
An gudanar da jana’iza ta gaba-daya ga mahaifiyarta Afraa, da mahaifinta Abdullah da kuma ‘yan uwanta hudu.
Suna daga cikin mutane 1,800 da aka san cewa sun rasu a girgizar kasar a Syria, kamar yadda bayanai suka nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...