Bayan umarnin kotu Buhari ya karbi bakuncin Emefiele

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a Aso Rock, Abuja.
 Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kotun kolin kasar nan ta yanke hukuncin dakatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina karɓar tsofaffin kudaden naira guda uku da aka sauyawa fasali.
 Kotun Kolin karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, ya yanke hukuncin na wucin gadi ne bayan da gwamnonin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar karar .
Talla
 Kotun kolin ta kuma ce ba dole ne gwamnatin tarayya da CBN su bari a cigaba da karɓar tsofaffin kudin har sai  ranar 15 ga Fabrairu Sanda ta yanke hukunci.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...