Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a Aso Rock, Abuja.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kotun kolin kasar nan ta yanke hukuncin dakatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina karɓar tsofaffin kudaden naira guda uku da aka sauyawa fasali.
Kotun Kolin karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, ya yanke hukuncin na wucin gadi ne bayan da gwamnonin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar karar .

Kotun kolin ta kuma ce ba dole ne gwamnatin tarayya da CBN su bari a cigaba da karɓar tsofaffin kudin har sai ranar 15 ga Fabrairu Sanda ta yanke hukunci.
