‘Yan fafutikar zaɓen 12 ga watan Yunin 1993 na sake haɗuwa – Ganduje

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce wasu ‘yan fafutikar zaɓen 12 ga watan Yunin 1993 da aka soke, na sake haɗuwa domin yin amfani da halin da ake ciki na sauya fasalin kuɗin ƙasar wajen yi wa dimoradiyyar ƙasar ƙafar-ungulu.

Gwamnan ya ce waɗannan mutane na ɓoye ƙansu a matsayin jam’iyyun da ba sansu ba tare da yin aiki da ɗan takarar shugabancin babbar jam’iyyar adawar ta PDP, domin ƙaƙaba wa talakawa dokar amfani da sabbin takardun kuɗi.
Kalaman gamnan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin hana Babban Bankin ƙasar CBN sake tsawaita wa’adin amfani da tsofin takardun kuɗin gdaga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Talla
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar Muhammad Garba, ya fitar Ganduje ya zargi Babban Bankin ƙasar da masu goyon bayansa kan sauya fasalin takardun kuɗin ƙasar da kasancewa masu tsanani wajen ƙaƙaba wannan doka da za ta ‘wahalar’ da mutane.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Duk kuwa da kiraye-kirayen ‘yan ƙasar ciki har da majalisar dokokin ƙasar da ƙungiyar gamnoni.
Ganduje ya kuma yi zargin cewa goyon bayan da – babbar jam’iyyar adawa ta PDP tare da ɗan takararta na shugaban ƙasar Atiku Abubakar – suke bai wa CBN kan tsarin ya nuna akwai haɗin baki tsakaninsu domin yi wa dimokradiyyar ƙasar ƙafar-ungulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...