Sojoji sun kubutar da Mutane 18 da akai safarar su daga Kano

Date:

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kuɓutar da mutum 18 da aka yi safarsu a unguwar Rijiyar Lemu da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano da ke arewacin Najeriya

 

A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce ta kama mutum biyu da take zargi da hannu wajen safarar mutanen.

 

Rundunar ta ce ta samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan da wani jami’insu ya ankarar da su kasancewa ‘yar uwarsa na daga cikin mutanen da aka yi safar tasu.

 

Sojojin ruwan sun ce sun miƙa mutanen tare da waɗanda ake zargin hannun hukumar da ke yaƙi da safarar bil-adama ta ƙasar domin ɗaukar mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...